Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Daily News Egypt ta bayyana cewa Nabil Al-Mallah shugaban tashar jiragen sama na Sharm El-Sheikh ya tarbi fasinjoji na farko da suka isa kasar don yawon bude ido daga kasar Burtaniya tun watan yulin da ya gabata.
Jaridar ta kara da cewa Khaled Al-Anany ministan yawon bude ido na kasar Masar ya gana da jakadan kasar Burtaniya a kasar Masar makonni biyu da suka gabata kafin Burtaniya da dage hanin da ta yiwa ‘yan kasar zuwa Masar.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne kasar ta Burtaniya ta sanya kasar Masar cikin jerin kasashen da ta hana ‘yan kasar zuwa saboda yadda cutar korona take yaduwa a cikinsu.
342/